Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2019

LABARAN SAFIYAR JUMA'AH 25/01/2019

Labaran Safiyar Jumma'a 25/01/2019CE - 18/05/1440AH. Cikakkun labaran  Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai dawo da martabar Najeriya da ta zube. Boko Haram sun kashe mutum 2 a Yobe bayan da sojoji suka tsere. Kabilar Ibo mazauna jihar Kano sun nuna goyon bayansu ga Ganduje. Dandazon mutane sun hallarci wurin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Buhari a jihar Enugu. Wasu yan fashi da makami sun kai farmaki a wani bankin Polaris da ke Oke Ejigbo, Ila Orangun da ke jihar Osun. Kotun daukaka kara ta maida wa Donald Duke takarar sa ta kujerar shugaban kasa a jam'iyyar SDP. Shugaba Buhari ya bayyana cewa, zai samar da tashar Jirgin kasa a jihar Kebbi. Wasu kungiyoyi na son kasashen Turai su sanya wa Obasanjo Takunkumin shiga kasashen waje. A jamhoriyar Nijar wani rikici ne ke neman barkewa a hukumar hajji da umara na kasar. Kasar Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowani dan takara a Najeriya. Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya,...

Zaben 2019: Atiku ya gama cin zaben 2019 – Buba Galadima

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takararsu a zaben 2019 ya gama lashe zaben saboda yadda ya samu karbuwa wajen al'ummar Najeriya. Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis. Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, wanda ke neman wa'adi na biyu. Buba Galadima ya ce suna godiya ga 'yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu a tarukan yakin neman zabe da ke gudana a fadin kasar. "Kuma idan dai kuri'ar dan Najeriya ita za ta tabbatar da cin zabe, to mun gama cin zabe," in ji shi. Ba zan nemi gafarar Buhari ba - Buba Galadima Buhari yana da matsala a Arewa - Buba Galadima Buhari da Atiku sun raba kan malaman Izala Har ila yau, ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya fi Shugaba Buhari tara jama'a a lokutan yakin neman zabe. Buba Galadima wanda a baya na hannun daman Shugaba Buhari ne kaf...

Kimiyya da fasaha

https://tukunyarmata5130.blogspot.com/2019/01/yadda-zakayi-rubutu-da-hausa-abiyaka.html?_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C8827616376