Skip to main content

Zaben 2019: Atiku ya gama cin zaben 2019 – Buba Galadima

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takararsu a zaben 2019 ya gama lashe zaben saboda yadda ya samu karbuwa wajen al'ummar Najeriya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis.
Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, wanda ke neman wa'adi na biyu.
Buba Galadima ya ce suna godiya ga 'yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu a tarukan yakin neman zabe da ke gudana a fadin kasar.
"Kuma idan dai kuri'ar dan Najeriya ita za ta tabbatar da cin zabe, to mun gama cin zabe," in ji shi.
Har ila yau, ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya fi Shugaba Buhari tara jama'a a lokutan yakin neman zabe.
Buba Galadima wanda a baya na hannun daman Shugaba Buhari ne kafin ya fara mara wa Atiku baya, ya yi zargin cewa Buhari yana amfani da kudi ne wajen tara jama'a.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa cewa kudi ne suka sa shi komawa wurin Atiku Abubakar, inda ya ce: "Buhari bai taba ba ni koda sisin kwabo ba, to idan shi a lokacin bai ba ni ba, to ya za a ce a yanzu wani zai saye ni."

Comments

Popular posts from this blog

Kimiyya da fasaha

https://tukunyarmata5130.blogspot.com/2019/01/yadda-zakayi-rubutu-da-hausa-abiyaka.html?_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C8827616376

KIWON LAFIYA it

Arewa Students Orientation Forum Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 30 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 21- Physiotherapy Daya ne daga cikin bangarorin da Medical Sciences yake da su. Kuma Bangare ne da yake ta'amulli da Kashi. Saboda haka wanda ya karanta Course din ana kidan shi ne da suna Physiotherapist (Wato likitan Kashi) Wuraren da zaka iya yin aiki da Degree a Physiotherapy:- 1. Animal physiotherapist 2. Higher education lecturer 3. Physiotherapist 4. Sports therapist 5. Acupuncturist 6. Chiropractor 7. Dance movement psychotherapist 8. Exercise physiologist 9. Health service manager 10. Health promotion specialist 11. Osteopath 12. Personal trainer A Nigeria Jami'o'i takwas ne kawai suke yin Degree na wannan Course din, ga Sunayen su:- 1. University of Lagos (UNILAG) 2. University of Benin (UNIBEN) 3. University of Ibadan (UI) 4. Bayero University Kano (BUK) 5. Bowen University (BU) 6. University ...

KARATUN LAFIYA

Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 31 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 23. Radiography 24. Medical Radiography and Radiological Science Menene Radiography, kuma su waye Radiographers, Sannan Su waye Radiologists ? Radiography ilimi ne na kimiyya da ake amfani dashi wajen daukar hoton cikin jikin sassan dan Adam dan a fahimci cutar da take damun shi. Ko kuma, Radiography ilimi ne na amfani da haske wajen gano cututtuka ta hanyar daukar hoto. Su kuma Radiologists Sune wadanda suke da wani training ko kwarewa ta musamman wajen fahimtar ko sanin cututtukan da wannan Photon da Radiographer ya dauka Inda su kuma Radiographers sune masana ko kwararru wajen daukar hoton cikin jikin marar lafiya dan su gano rauni ko cutar da ke cikin jikin ta hanyar wannan hoton. Wuraren da zaka iya yin aiki idan ka karanta Radiography:- 1. University teaching hospitals throughout the country 2. Federal medical centers nationwide 3. State hospitals 4....