Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 31 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 23. Radiography 24. Medical Radiography and Radiological Science Menene Radiography, kuma su waye Radiographers, Sannan Su waye Radiologists ? Radiography ilimi ne na kimiyya da ake amfani dashi wajen daukar hoton cikin jikin sassan dan Adam dan a fahimci cutar da take damun shi. Ko kuma, Radiography ilimi ne na amfani da haske wajen gano cututtuka ta hanyar daukar hoto. Su kuma Radiologists Sune wadanda suke da wani training ko kwarewa ta musamman wajen fahimtar ko sanin cututtukan da wannan Photon da Radiographer ya dauka Inda su kuma Radiographers sune masana ko kwararru wajen daukar hoton cikin jikin marar lafiya dan su gano rauni ko cutar da ke cikin jikin ta hanyar wannan hoton. Wuraren da zaka iya yin aiki idan ka karanta Radiography:- 1. University teaching hospitals throughout the country 2. Federal medical centers nationwide 3. State hospitals 4....
Muryar arewa 24 Munbude wannan Gidan Domin wayer dakan Al ummar arewa dama Nigeria gabaki daya.