Skip to main content

Posts

Featured post

KARATUN LAFIYA

Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 31 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 23. Radiography 24. Medical Radiography and Radiological Science Menene Radiography, kuma su waye Radiographers, Sannan Su waye Radiologists ? Radiography ilimi ne na kimiyya da ake amfani dashi wajen daukar hoton cikin jikin sassan dan Adam dan a fahimci cutar da take damun shi. Ko kuma, Radiography ilimi ne na amfani da haske wajen gano cututtuka ta hanyar daukar hoto. Su kuma Radiologists Sune wadanda suke da wani training ko kwarewa ta musamman wajen fahimtar ko sanin cututtukan da wannan Photon da Radiographer ya dauka Inda su kuma Radiographers sune masana ko kwararru wajen daukar hoton cikin jikin marar lafiya dan su gano rauni ko cutar da ke cikin jikin ta hanyar wannan hoton. Wuraren da zaka iya yin aiki idan ka karanta Radiography:- 1. University teaching hospitals throughout the country 2. Federal medical centers nationwide 3. State hospitals 4....
Recent posts

LIKITANCHI

Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 32 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 25. Veterinary Medicine Shima daya ne daga cikin bangarorin da Medical Sciences yake dasu. VETERINARY MEDICINE ilimi ne na kimiyya da wanda ya karantashi yake amfani dashi wajen gano da magance duk wasu cututtuka da suka samu dabbobi ko kuma idan sukaji rauni, haka kuma da basu matakan kariya daga kamuwa da cututtukan. Doctor of Veterinary Medicine (Wato likitan dabbobi) shima kamar likitan mutane ne, Programme ne da ake share Shekara 6 ana yin sa a Jami'a. Hakanan kuma kwas ne mai wahala, dan wasu ma suna ganin yafi Medicine and Surgery wahala, kasancewar wadanda zakayi ta'ammali dasu a wannan bangaren ba mutane bane, kuma bazasu iya yimaka bayanin abunda ke damun su ba, wannan dama sauran wasu abubuwan suka sanya wasu ke ganin yafi likitan mutane wahala. Wanda ya karanta wannan Course din ana kiransa ne da suna Veterinarian ko kuma Doctor Of Veter...

KIWON LAFIYA it

Arewa Students Orientation Forum Musan Tsangayoyin Mu Kashi Na 30 (09-02-2019) ~Medical Sciences -Bangarorin da Medical Sciences yake da su 21- Physiotherapy Daya ne daga cikin bangarorin da Medical Sciences yake da su. Kuma Bangare ne da yake ta'amulli da Kashi. Saboda haka wanda ya karanta Course din ana kidan shi ne da suna Physiotherapist (Wato likitan Kashi) Wuraren da zaka iya yin aiki da Degree a Physiotherapy:- 1. Animal physiotherapist 2. Higher education lecturer 3. Physiotherapist 4. Sports therapist 5. Acupuncturist 6. Chiropractor 7. Dance movement psychotherapist 8. Exercise physiologist 9. Health service manager 10. Health promotion specialist 11. Osteopath 12. Personal trainer A Nigeria Jami'o'i takwas ne kawai suke yin Degree na wannan Course din, ga Sunayen su:- 1. University of Lagos (UNILAG) 2. University of Benin (UNIBEN) 3. University of Ibadan (UI) 4. Bayero University Kano (BUK) 5. Bowen University (BU) 6. University ...

LABARAN YAMMACIN JUMA'AH 08/02/2019

Labaran Yammacin Jumma'a 08/02/2019CE - 03/06/1440AH. Cikakkun labaran Wasu fusatattun matasa sun kashe wani matashi bayan ya kashe mahaifiyarsa a jahar Enugu. 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato mai suna Honorabul Sani Yakubu. Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta dauki alkawarin samar da hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan. Atiku Abubakar ya yi zargin cewa akwai wani makirci da ake kullawa na son kama manyan hadimansa kafin zabe mai zuwa. Zargin sace N4.6bn: Kotu ta wanke tsohon gwamnan jihar Oyo, Rasheed Ladoja  da kwamishinansa. Olu Falae ya bar harkar siyasa kwana daya bayan SDP ta zabi Buhari a matsayin dan takararta. Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon sakataren gwmnatin tarayya Babachir Lawan a ranar Talata. Zaben 2019: Ministan Ilimi ya ba da umarnin garkame kwalejojin gwamnatin tarayya 109 don gudun ko-ta-kwana. Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya ce Najeriya ta gama da Boko Haram,...

LABARAN YAMMACIN YAU ALHAMIS 7/2/2019

Labaran Yammacin Alhamis 07/02/2019CE - 02/06/1440AH. Cikakkun labaran BARKANMUDA YAMMA Jam'iyyar SDP ta yi wa shugaba Buhari mubaya'a, ta ce za ta mara masa baya a zaben shugaban kasa. Kotu ta tsige Sanata David Ummaru a matsayin dan takarar APC, inda ta sanar da Mohammed Musa 313 a matsayin halastaccen dan takara. Hukumar INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91. Fadar Shugaban kasa ta ce ta gamsu da karin bayanin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi game da gargadin da ya yiwa kasashen waje masu niyyar yin katsalandan a zaben Najeriya. Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Birigadiya Janaral Sani Usman Kukasheka ya sanar da ajiye aikinsa domin kashin kanshi. Mutane 2 sun rasa rayukansu a turmutsitsin gangamin yakin neman shugaban kasa na APC a Jalingo jihar Taraba yau. A karshe dai gwamnatin Kano ta bude filin wasa na Sani Abacha domin PDP ta gudanar da yakin neman zabe. An sake zaben Ayuba Wabba a matsayin shu...

ASSU suspend nationwide strike

The Academic Staff Union of Universities, ASUU, has officially suspended a strike it commenced three months ago. The union directed university lecturers to resume duty from tomorrow, February 12. The suspension of the strike was announced on Thursday evening after a meeting with between the ASUU leadership and a government delegation led by labour minister, Chris Ngige. The ASUU delegation was led by its president, Abiodun Ogunyemi, who announced the suspension of the strike. At the meeting, a memorandum of action was signed by the two parties. Mr Ngige had earlier said the government had resolved the eight contentious issues that led to the strike. He said some of the items have been implemented. Okowa Campaign AD Mr Ngige said the union agreed with the government that N25 billion naira will be released for the revitalization of public universities. He said visitation panels have been constituted and will commence work on March 2. ASUU embarked on an indefinite strike on Nove...

LABARAN SAFIYAR JUMA'AH 25/01/2019

Labaran Safiyar Jumma'a 25/01/2019CE - 18/05/1440AH. Cikakkun labaran  Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai dawo da martabar Najeriya da ta zube. Boko Haram sun kashe mutum 2 a Yobe bayan da sojoji suka tsere. Kabilar Ibo mazauna jihar Kano sun nuna goyon bayansu ga Ganduje. Dandazon mutane sun hallarci wurin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Buhari a jihar Enugu. Wasu yan fashi da makami sun kai farmaki a wani bankin Polaris da ke Oke Ejigbo, Ila Orangun da ke jihar Osun. Kotun daukaka kara ta maida wa Donald Duke takarar sa ta kujerar shugaban kasa a jam'iyyar SDP. Shugaba Buhari ya bayyana cewa, zai samar da tashar Jirgin kasa a jihar Kebbi. Wasu kungiyoyi na son kasashen Turai su sanya wa Obasanjo Takunkumin shiga kasashen waje. A jamhoriyar Nijar wani rikici ne ke neman barkewa a hukumar hajji da umara na kasar. Kasar Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowani dan takara a Najeriya. Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya,...

Zaben 2019: Atiku ya gama cin zaben 2019 – Buba Galadima

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takararsu a zaben 2019 ya gama lashe zaben saboda yadda ya samu karbuwa wajen al'ummar Najeriya. Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis. Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, wanda ke neman wa'adi na biyu. Buba Galadima ya ce suna godiya ga 'yan Najeriya saboda irin goyon bayan da suke samu a tarukan yakin neman zabe da ke gudana a fadin kasar. "Kuma idan dai kuri'ar dan Najeriya ita za ta tabbatar da cin zabe, to mun gama cin zabe," in ji shi. Ba zan nemi gafarar Buhari ba - Buba Galadima Buhari yana da matsala a Arewa - Buba Galadima Buhari da Atiku sun raba kan malaman Izala Har ila yau, ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar ya fi Shugaba Buhari tara jama'a a lokutan yakin neman zabe. Buba Galadima wanda a baya na hannun daman Shugaba Buhari ne kaf...

Kimiyya da fasaha

https://tukunyarmata5130.blogspot.com/2019/01/yadda-zakayi-rubutu-da-hausa-abiyaka.html?_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C8827616376