
Labaran Safiyar Jumma'a 25/01/2019CE - 18/05/1440AH. Cikakkun labaran
Alhaji Atiku Abubakar ya ce zai dawo da martabar Najeriya da ta zube.
Boko Haram sun kashe mutum 2 a Yobe bayan da sojoji suka tsere.
Kabilar Ibo mazauna jihar Kano sun nuna goyon bayansu ga Ganduje.
Dandazon mutane sun hallarci wurin kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Buhari a jihar Enugu.
Wasu yan fashi da makami sun kai farmaki a wani bankin Polaris da ke Oke Ejigbo, Ila Orangun da ke jihar Osun.
Kotun daukaka kara ta maida wa Donald Duke takarar sa ta kujerar shugaban kasa a jam'iyyar SDP.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, zai samar da tashar Jirgin kasa a jihar Kebbi.
Wasu kungiyoyi na son kasashen Turai su sanya wa Obasanjo Takunkumin shiga kasashen waje.
A jamhoriyar Nijar wani rikici ne ke neman barkewa a hukumar hajji da umara na kasar.
Kasar Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowani dan takara a Najeriya.
Mahaifiyar fitaccen dan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa, ta rasu.
Middlesbrough ta dauki tsohon dan wasan Chelsea John Mikel Obi a wata yarjejeniya har zuwa karshen kakar bana.
Wane Labarine Yafijan Hankalinka/Ki
Comments
Post a Comment