Labaran Yammacin Alhamis 07/02/2019CE - 02/06/1440AH. Cikakkun labaran
BARKANMUDA YAMMA
Jam'iyyar SDP ta yi wa shugaba Buhari mubaya'a, ta ce za ta mara masa baya a zaben shugaban kasa.
Kotu ta tsige Sanata David Ummaru a matsayin dan takarar APC, inda ta sanar da Mohammed Musa 313 a matsayin halastaccen dan takara.
Hukumar INEC ta saki samfurin takardan kuri'a dauke da jam'iyyu 91.
Fadar Shugaban kasa ta ce ta gamsu da karin bayanin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi game da gargadin da ya yiwa kasashen waje masu niyyar yin katsalandan a zaben Najeriya.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Birigadiya Janaral Sani Usman Kukasheka ya sanar da ajiye aikinsa domin kashin kanshi.
Mutane 2 sun rasa rayukansu a turmutsitsin gangamin yakin neman shugaban kasa na APC a Jalingo jihar Taraba yau.
A karshe dai gwamnatin Kano ta bude filin wasa na Sani Abacha domin PDP ta gudanar da yakin neman zabe.
An sake zaben Ayuba Wabba a matsayin shugaban kungiyar kwadago, NLC
Hukumar INEC ta tabbatar cewa Jam’iyyar APC ba ta da dan takara a Jihar Rivers.
Jiragen yaki na Isra'ila sun kai hari ta sama da bama-bamai kan sansanin dakarun Hamas na Izzeddin Al Kassam.
An sanya dokar ta baci sakamakon wata mummunar gobarar daji da ta kama dazukan yankin tsaunukan kudu dake kusa da garin Nelson a kasar New Zealand.
Wane labari yafi daukar hankalinku?
Comments
Post a Comment